Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Taron Kolin Kasashen Nahiyoyin Afirka Da Amurka Ta Kudu A Abuja


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya yayi kiran da a karfafa hulda a tsakanin Afirka da Amurka ta kudu, a yayin da shugabannin nahiyoyin biyu suka hallara a Abuja, babban birnin Nijeriya.

A lokacin da yake jawabi ga shugabannin kasashe da gwamnatocin da suka hallara domin taron kolin farko na kasashen Afirka da Amurka ta kudu, Cif Obasanjo ya ce tilas ne wannan taron ya zamo harsashin farko na kawance mai dorewa.

Wani kakakin wadanda suka shirya taron kolin, ya ce batutuwan da za a tattauna zasu kunshi zuba jari, makamashi da albarkatun kasa da kuma zaman lafiya da tsaro. Ya ce shugabannin kasashen Afirka dake halartar taron su na shirin tattauna rikicin yankin Darfur na kasar Sudan a yau alhamis.

Kasashen nahiyar Amurka ta kudu kamar Venezuela da Brazil su na kokarin karfafa muradunsu a Afirka, kamar dai irin matakan da kasar Sin da Kungiyar Tarayyar Turai suka dauka kwanakin baya na karfafa huldar tattalin arziki da ta siyasa da nahiyar.

Masu shirya taron suka ce kasashen Afirka fiye da hamsin da kuma kasashe 12 a Amurka ta kudu sun tura wakilansu zuwa taron.

XS
SM
MD
LG