Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta Kife Sun Yi Barazanar Kai Karin Hare-Hare A Kan Cibiyoyin Mai A Nijeriya


'Yan ta-kifen Nijeriya sun yi barazanar kai karin hare-hare a kan cibiyoyin mai a bayan da suka sace ma'aikatan mai 'yan kasashen waje su hudu a yankin Niger Delta.

A yau jumma'a Kungiyar kwato 'yancin Niger Delta mai suna MEND a takaice, ta dauki alhakin sace 'yan kasar Italiya uku da wani dan kasar Lebanon daya jiya alhamis. 'Yan bindiga sun kuma kashe mutum guda a harin kan wata tashar lodin mai zuwa kasashen waje mallakar kamfanin AGIP na Italiya.

Jami'an mai a Nijeriya sun ce sun tuntubi mutanen da suka sace ma'aikatan a Jihar Riverssu na kokarin tsara yadda za a sako su.

Sace mutane domin neman kudin fansarsu ya zamo ruwan dare a yankin na Niger Delta, inda akasarin mutane suke zaune cikin talauci duk da dimbin arzikin man fetur na yankin.

Har ila yau 'yan ta kife sun kai hare-hare a kan cibiyoyin mai da dama a yayin da suke kokarin ganin an bai wa yankin karin kaso na arzikin man da yake samarwa kasar baki daya.

XS
SM
MD
LG