Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Amirka ta kara dala miliyon 100 don yaki da murrar tsuntsaye


Gwamnatin Amirka ta bada sanarwar a ranar goma sha daya ga wannan wata na Disamba cewa tun daga watan janairu zuwa yanzu ta kashe zata kara dala Miliyon 100 a matsayin taimakon da take baiwa kashen duniya somin yaki da cutar mashasharan Tsuntsaye da kuma annobar cututtukan dan Adam. Amirka ta fadi hakan ne a birnin Bamako na kasar Mali a wajen taron karawa juna Ilmi akan yaki da cutar murrar tsuntsaye, taron da gwamnatin kasar Mali ta taimaka aka shirya shi tare da kungiyar Tarayyar Turai da kuma kungiyar tarayya kasashne Afrika.

Wakilin gwamnatin Amirka na musamman mai kula da mashassharar Tsuntsaya da kuma na dan Adam, John E lange ne ya bada wannan sanarwa cewa gwamnatin Amirka ta kara adadin da ada ta yi niyar bayarwa na dala miliyon 334, abinda ta fara sanarwa a watan janairu a babban taron da akayi a birin Beijin na kasar China, daga baya ta kara adadin zuwa dala miliyon 362 a watan Yuni sannan daga baya ta kara wannan kudi zuwa dala miliyon 434, Karin dala miliyon 100 kanan.

Wannan Karin ya hada da dala miliyon 36 da cibiyar rayarwa ta kasa da kasa ta amirka da kuma dala miliyon 36 daga ma’aikatar lafiya da kula a al’uma na amirka. Tunin kuma gwamnatin ta kulla wata yarjejeniyar dala bada agajin dala miliyon 324 tsakaninta da sauran kasashe dake bada agaji domin yaki da wannan mammunan kwayar cuta ta nau’in H5N1.

XS
SM
MD
LG