Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filin A Bari Ya Huce Ya Tuna James Brown


Ranar litinin 25 ga watan Disamba, 2006, watau ranar Kirsimeti da asubahi, mashahurin mawakin Amurka bakar fata James Brown, wanda sunansa ya karade fadin duniya, ya bar duniya a birnin Atlanta a Jihar Georgia, a bayan da aka kwantar da shi ranar lahadi dauke da ciwon hakarkari.

Filin "A Bari Ya Huce.." ya tuno da rayuwar marigayi James Brown ta hanyar duba irin gudumawar da ya bayar ga wakoki, da kuma kyautata rayuwar bakar fata, musamman matasa.

An haifi James Brown ranar 3 ga watan Mayun 1933 a kusa da garin Barnwell dake Jihar Carolina ta Kudu. Iyayensa matalauta ne sosai. Mahaifinsa yana shiga jeji ya debo karo da yake sayarwa domin su samu abin ci.

James Brown da mahaifinsa Joe Brown sun koma Augusta a Jihar GA bayan da mahaifiyarsa ta bar gidan lokacin yana da shekaru 7. Allah Ya halicce shi da basira da kwazo da kuma aiki tukuru: ya koyi yadda ake buga ganga da piano da gita yayin da yake taya mahaifinsa aiki a gona, yake kuma aikin shushaina.

Kafin ya cika shekaru 13 da haihuwa James Brown ya kafa kungiyarsa ta mawaka, daga baya ya shiga cikin wata kungiyar mai suna "The Flames" suna zagaya makarantu da gidajen wasanni da duk inda aka gayyace su suna waka don a biya su. A cikin wakokin da suke yi har da wata mai suna "Please please please", wakar da ta fara fito da sunan James Brown a duniya.

A 1986, James Brown na daya daga cikin mawakan farko da aka shigar da su cikin dakin tarihin mawakan Rock And Roll. Im ban da wani mawaki mai suna Elvis Presley, babu wani wanda wakokinsa suka kai yawan na James Brown a cikin jerin wakokin da suka fi farin jini a Amurka. Wakokinsa har 94 suka shiga cikin jerin wakoki 100 da aka fi yayinsu a lokuta dabam dabam a nan Amurka.

An bai wa James Brown kyautar lambar yabon mawaka ta Grammy a zaman mutumin da ya shafe rayuwarsa yana bayar da gudumawa, kuma daga baya yayi magana a kan yadda yayi kokarin gabatar da sakon karfafa guiwa a duk tsawon rayuwarsa.

Har ya zuwa karshen rayuwarsa, James Brown ya ci gaba da wasa tare da taimakawa mutanen garinsu. Kwanaki uku kafin mutuwarsa ma, ya halarci bukin da ya saba shiryawa kowace shekara na rarraba kyautar kayayyakin wasa ga yara a Augusta.

A da yayi shirin cewa lahadin nan watau jajiberen sabuwar shekara, zai yi wasa a New York, amma Allah bai nufa zai ga wannan rana ba.

James Brown ya rasu yana da shekaru 73 da haihuwa.

(Za a iya sauraron cikakken shirin, tare da hira da shi marigayin idan an matsa wurin da aka rubuta Saurari shirin a saman wannan labari).

XS
SM
MD
LG