Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rataye Saddam Husseini


An zartas da hukumcin kisa a kan hambararren shugaban kasar Iraqi, Saddam Husseini, bisa laifuffukan cin zarafin bil Adama.

Yau asabar da asubahi agogon Iraqi ne aka rataye Saddam Husseini a Bagadaza, kwanaki hudu a bayan da babbar kotun Iraqi ta yi watsi da daukaka karar da ya shigar.

A ranar 5 ga watan Nuwamba aka yanke hukumcin kisa a kan tsohon shugaban bisa laifin bayar da umurnin kashe mutane 148 'yan mazhabin Shi'a a wani kauye cikin shekarar 1982, a bayan wani yunkurin da ya ci tura na kashe shi a kauyen.

Gidan telebijin na Iraqi ya nuna hoton bidiyo na rataye Saddam, inda aka ga wasu mutane da dama da suka rufe fuskokinsu, sun taho da Saddam cikin sarka zuwa dandalin da aka rataye shi din. daga nan aka daura masa igiya a wuya.

An ga alamun kwanciyar hankali a fuskar Saddam, wanda ya ki yarda a rufe masa fuska da kyalle, kafin rataye shi.

Daga baya an ga hotunan bidiyo na gawar Saddam cikin farin likkafani a gidan telebijin na Iraqi. An ga kansa, wanda ba ya rufe a cikin likkafanin, a karkace (alamar wuyarsa ta karye).

An kashe Saddam Hussein a wata tsohuwar hedkwatar hukumar leken asirin soja dake wata unguwar 'yan mazhabin Shi'a ta Bagadaza mai suna Kazimayah.

Jami'an Iraqi su na tattaunawa da iyalan marigayin a kan yadda za a binne shi.

XS
SM
MD
LG