Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samo wani Sabon maganin Rigakafin cutar Murrar Tsuntsaye


An fara jarrwa wani maganin rigakafin cutar murrar tsuntsaye dake kama ‘yan Adam na farko a duniya a ranre 21 ga watan Disamba na 2006 ranar da aka gwada maganin kan wani wanda ya yarda zai bada kansa a jarrabashi da maganin cutar a cibiyar nazarin cututtuka ta Amirka wata NIH a garin Bethesda a jahar Maryland anan Amirka. Masana ilmin kimiyya daga wata cibiyar nazarin magaungunan rigakafi, da likitoci a cibiyar nazarin cututtuka masu yado sunce kwayar maganin bai kunshi wani jinsi na cutar murrar tsuntsayen ba.

Shi wannan magani dabam yake da sauran magungunan rigakafin cutar murrar tsuntsaye wadadna ake hadasu tare da sanya kwayoyin cutar murrar cikin kwan kaji ko naman kafin kafin a kyaleta ta kosa ta zama cutar sannan a jarraba shi jikin dan adam amatsayin wani magani da zai kashe kwayar cutar.

Darektan cibiyar jarraba magungunan rigakafin kwayoyin cutar, Dr. Gary Nabel yace samun wani maganin rigakafin cutar murrar tsuntsaye ta nau’in H5N1 zai samara da wata sabuwar hanyar yaki da wannan cuta da kuma kara tara maganin saboda zama cikin shirin ko ta kwana, lokacin da cutar zata bullo ba shiri nan gaba.

XS
SM
MD
LG