Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An saki wani hoton vidiyo na ma'aikatan kanfani a Iraq


An saki wani hoton bidiyo na ma’aikatan wani kamfanin tsaro na kasashen yammacin turai da aka sace kimanin sati bakwai da suka wuce a Iraqi. Wadanda ke hannu dai, Amurkawa hudu ne da wani mutumin Australiya guda daya, kuma daya bayan daya aka nuna su a wani dandalin yanar gizo na intanet, kuma aka rabawa kafofin yada labaran yamma.

Dukkan mutum biyar din dai sunce ana kula dasu yadda ya kamata, kuma da alamu suna cukin koshin lafiya. Daya daga cikin wadanda aka sace din yace an gaya masu ba za a sake su ba, sai an saki fursunonin Iraqi dake hannun Amurka da Birtaniya. Vidiyon din dai bai nuna wadanda suka sace mutanen ba.

Mutanen dai wadanda ke aiki a wani kamfani dake da cibiya a kasar Kuwait, mai suna Crescent Security, suna rakiyar wani ayari ne, lokacin da wadansu mutane dake sanye da kayan ‘yan sandan Iraqi, suka kamesu a birnin Basra, rana 16 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata. Babu dai wata kungiya guda daya da ta fito ta dauki alhakin wannan aiki.

XS
SM
MD
LG