Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gwabza Fada A Kudancin Somaliya


Sojojin taron dangi na Somaliya da Ethiopia sun gwabza da mayakan Islama a kudancin Somaliya, inda masu kishin addinin suka yi tunga bayan da suka fice daga babban birnin kasar.

Wani kwamandan sojojin gwamnatin riko ta Somaliya da ’yan’uwan sojoji sun ce ana gwabzawa domin neman kwace Ras Kamboni. Masu kishin addini sun koma yankin a bayan da suka bar tsohuwar tungarsu dake Kismayo a kudu da Mogadishu kwanakin da suka shige.

Magoya bayan Kungiyar Kotunan Islama ta Somaliya sun bar Mogadishu a makon jiya a bayan da sojojin Somaliya da na Ethiopia suka yi wa birnin tsinke. A watanni shidan da suka shige dai masu kishin addinin sun fadada ikonsu zuwa akasarin kudancin kasar.

Kasar Somaliya ta fada cikin fitina tun lokacin da kungiyoyin sojojin sa kai suka hambarar da gwamnatin marigayi Mohammed Siad Barre a 1991.

XS
SM
MD
LG