Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Shabbab ta Somalia tafi ban tsoro a kasar


Kafin kungiyar ‘yan kishin Islama ta kasar Somaliya ta rasa ikon da take dashi a yawancin garuruwan kudancin kasar Somaliya, a wata kungiyar da ba’a san da ita sosai ba ta matasa ‘yan tsagera dake kiran kanta kungiyar Shabbab, ta kunno kai sosai. Ita dai wannan kungiyar wakilanta biyu matsa ‘yan shekara 18 da haifuwa, Abdi da Hassan sunyi magana da Muryar Amirka inda suka yi maganar da ba wata kafar yada labarai da ta san da ita ada.

Wadannan ‘yan kasar Somalian sun fadawa Murayar amirka cewa a cikin watanni 6 da da kungiayr ‘yan kishin Islamar kasar take rike da ikon birnin Mogadishu, ko da wasa akaga alamar wani dan wannan kungiyar da Shabbab, wadda mabiya bayanta suke sanye da wani kenllen mai launin Ja da Fari a wuyansu, mutane suna tsorata su shiga gudun tsira da rai. Mutanen kasar Somaliyar basu san wani abu sosai game da wannan kungiaya ba, ko yadda take gudanar da ayyukanta.

To amma da dama sunji labarin kafuwar kungiyar a wajejen shekara ta dubu biyu da hudu a matsayin wata kungiyar cikin gida ta‘yan tsagera wacce take daukar yara kananan ayyukan Jihadi, ko yaki da makiya addinin Islama. Wani tsohon dan wannan kungiya kuma dan shekarau 18 da haifuwa mai suna Abdi ya ce kungiyarsu tana yin taka tsantsan sosai wajen daukar wadanda zasu rika mata ayyukan jihadi. Ya ce sai sun binciki tarihin matshi da kuma irin akidunsa domin tabbatar da cewa shi ba dan liken asiri bane. Kiran da kungiyar tayi akan a makiya addinin Islama ya hada da kira ayi yaki domin kare diyaucin kasar Somalia.

Haka kuma wani tsohon dan kungiyar dan shekaru 27, wanda ya bayyana sunansa Hassan yace irin kiranda wannan kungiyar takewa ‘yan kasar Somalia, ba kira bace da duk wani talaka, ko maras galihu zai ki amsawa. Hassan yace ya shiga wannan kungiyar da Shabban tare da wasu darurruwan matsa a watan Yuni na shekarar bara jim kadan bayan da sojojin ‘yan kishin Islamar Somaliya suka kame birnin Mogadishu.

Hassan ya baiyana yadda kungiyar Shabbab ta daukeshi sannan ta kaishi wani toshon ofishin ‘yansandan wanda aka mayar dashi sansanyin horaswa mai suna Fish Tafico inda aka horas dashi. Wannan sansanin yana zaman daya daga cikin sansanonin horaswar wannan kungiyar. Yace a sansanin ana rarraba wadanda aka dauka cikin kanannan kungiyoyi, sannan kowace kungiya ana mata horo mai tsanani domin su ‘yan kungiyar su saje da irin wahalolin da zasu fuskanta a bakin daga.

Duk da haka Hassan ya tabbatar da zargin da Ethopia da gwamnatin somalia sukayi cewa mayakan kotunan islamar sun dauki sojan haya domin su taya su yaki. Hassan yana cikin wani ayari dake kusa da garin Bur Hakaba mai tazaran kilomitoci daga helkwatar gwamnatin Somalia sai samun goyon bayan Ethopia inda aka yi dauki ba dadi na watan Disambar bara. Yace akwai larabawa 25 wadanda sukayi yaki tare da shi da kuma wasu ‘yan kungiyar Shabbab.

Duk da haka yace bai san ko daga wace kasace wadannan larabawan suka fito ba, kuma da dama daga cikinsu suna magana da harshen somaliyanci. Shi kuma Abdi yace an koya musu yadda zasu rika yin bama bamai na gefen hanya wanda zasu rika binnewa, da wadanda zasu rika sanyawa cikin mota da kuma yadda zasu sa falmarar kunan bakin wake dake da nakiyoyin domin su tarwatsa gungun mutane. Yace wadanda suka horas dashi sun hada da Somaliyawa da kuma Iritawan Eritiriya.

XS
SM
MD
LG