Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Rikon Kwarya na Somaliya, Abdullahi Yusuf ya shiga Mogadishu


Shugaban Rikon Kwarya na Somaliya, Abdullahi Yusuf ya shiga Mogadishu, babban birnin Kasar, a karon farko tun da ya shiga Office kimanin shekaru biyu da suka wuce. Ministan harkokin Wajen Somaliya, Isma’el Mohammed Hurreh, ya baiyana shigar Shugaban Mogadishu a yau Litinin, a matsayin wani abin tarihi, wanda ya tabbatar da kafuwar gwamnati a hedkwatarta.

Gwamnatin dai bata da wani karfi ko iko, har zuwa watan jiya, lokacin da kasar habasha ta taimaka mata wajen korar dakarun masu kishin musulunci daga birnin, da sauran garuruwan da suka mamaye. Har yanzu da babu kwanciyar hankali sosai a Mogadishu, mayakan sa kai ke kaiwa sojojin Habasha harin sari ka noke tsakanin Asabar da lahadi.

A wani musayar wuta da aka yi ma, an kashe mutum hudu, biyu daga cikinsu farar hula. Gwamnatin ta Somaliya da dakarun Habasha suna ci gaba da farautar mayakan sa kai na masu kishin Islama, a kewayen Ras Kimboni, dake kudancin kan iyakar kasar da Kenya.

XS
SM
MD
LG