Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyalai Da Abokai Da 'Yan'uwa Sun Yaba Da Halin Marigayi Ahmad S. Nuhu


Iyalai da 'yan'uwa da kuma abokan marigayi Ahmad S. Nuhu, sun ci gaba da bayyana irin kyawawan halaye na marigayin kafin rasuwar ranar litinin 1 ga watan janairun 2007, a wani hadarin motar da ya faru a tsakanin Azare da Kano.

A cikin kashi na biyu na shiri na musamman domin tunawa da marigayi, mun faro da jin bayanin mai dakinsa, Hajiya Hafsat, wadda ta bayyana godiyarta ga Allahu Subhanahu wa Ta'ala a saboda irin shaida da Ahmad Nuhu ya samu, da kuma irin kauna da jama'a suka nuna mata kan wannan rashi.

Ko bayan ita Hajiya Hafsat, Ali Nuhu, Sa'adiya Mohammed (Gyale), Sadiq Ahmed, Sadiq Mafia, Maryam Mashahama (Maryam Baba Danfulani), Lawal Ahmed, Mansur Sadiq, Safiya Musa Bukur da Tahir Ahmed, sun yi magana kan marigayin a cikin wannan kashi na biyu.

Idan ana son sauraro, ko kuma kofen wannan kashi na biyu na shirin, sai a matsa rubutun dake saman wannan labarin.

Allah Ya jikan Ahmad S. Nuhu, Ya gafarta masa. Allah Ya bada wadanda ya bari a baya hakurin jure wannan rashi, amin summa amin.

XS
SM
MD
LG