Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sace wani dan aikin diplomasiyyar Iran a Iraq


A kasar Iraq wasu ‘yan bindiga saye da kakin soji sun sace wani ma’aikacin diplomasiyyar kasar Iran a Iraq. Wani mai magana na yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran yace suna dora alhakin kama wannan jami’I wanda aka sace shekaranjiya lahadi a gundumar karrada, akan amirka kuma lafiyarsa tana hannun Amirka.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran din yace wadanda suka kama ma’aikacin nasu suna aiki ne a ma’aikatar tsaron kasar Iraq wacce ke karkashin jagorancin rundunar sojin Amirka. Wani mai magana da yawun rundunar sojin Amirka ya musanta cewa Amirka tana da wani hannu wajen sace wannan ma’aikacin diplomasiyyar Iran. Jami’an kasar Iraq sunce wadanda suka sace dan diplomasiyyar sun je ne cikin motoci suka tare motar ma’aikacin diplomasiyyar a wani lardi na ‘yan Shi’a.

A halin da ake ciki kuma firayi ministan Iraq Nouri Al Makliki ya roki kwamandodin rundunar sojin kasarsa akan su hanzarta shirye shiryen kai farmakin tsaro da zuwa cikin birnin bagadaza. Wani sabon shirin tsaro da aka shirya a birnin zai kunshi sojoji dubu 90 wadanda zasu rika sintirin tsaro a sassan birnin da yankunan dake makobtaka ta shi.

XS
SM
MD
LG