Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Falasdinawa Masu Adawa Da Juna Sun Cimma Yarjejeniya


Kungiyoyin Falasdinawa na Hamas da Fatah sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kai, a wani yunkurin kawo karshen tashin hankali a tsakaninsu da kuma takunkumin dake neman karya yankinsu.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas na kungiyar Fatah, da shugaban Hamas Khaled mashaal, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar yau alhamis a gaban Sarki Abdullahi na Sa'udiyya. Sarkin shine ya karbi bakuncin tattaunawar neman sulhu a tsakanin bangarorin biyu a birnin Makka.

An fara tattaunawa jiya laraba, kuma a yau alhamis sassan biyu sun cimma matsaya a kan yadda za a rarraba mukaman ministoci. Sai dai ba a san ko Hamas ta yarda da bukatun kasashen waje na yin watsi da tashin hankali a zaman manufa, da amincewa da kafuwar Isra'ila a zaman kasa, da kuma mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma a baya da kasar ta bani Yahudu ba.

Falasdinawa su na fata kafa gwamnatin hadin kai zai sa kasashen waje masu bayar da agaji su maido da agajin nasu da suka tsinke a bayan da Hamas ta hau kan mulki a shekarar da ta shige.

An kashe Falasdinawa fiye da casa'in a fada tsakanin kungiyoyin Hamas da Fatah tun cikin watan Disamba.

XS
SM
MD
LG