Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

kungiyyin adawa a Najeriya sun bijirewa EFCC


Kungiyoyin Adawa a Nigeria sunyi fatali da gargadin da hukumar yaki da zarmiya ta kasar Efcc ta yi musu cewa kadda su gabatar da sunan wasu ‘yan takaransu saboda tana zarginsu da aikata rashawa da cin hanci. A wannan mako ne hukumar yaki da zarmiya da cin hanci, ta EFCC ta bada rahoto da jerin sunayen ‘yan takaran mukamai daban daban su 130 inda ta ce basu cancanci rike wani mukami ba saboda hannu da suke da shi karbar rashawa da cin hanci.

Fitacce daga cikin ‘yan takaran shine mataimakin shugaban Nigeria Alh. Atiku abubakar wanda yake takarar shugabancin Nigeria a karkashin inuwar jam’iyar AC. Mataimakin shugaban Nigerian yayi barazanar zaiyi karar hukumar Efcc kuma jam’iyarsa ta AC tace zatayi fatali da wannan gargadi na Efcc, kuma dan takaranta zai ci gaba da tsayawa.

Jam’iyar ta zargi shugaba OBJ da laifin yunkurin hana Atiku tsayawa zabe. A shakara da ta wuce ne, Atiki abubakar ya yi tsayin daka na hana OBJ cigaba da rike karagar mulkin kasar a karo na uku.

XS
SM
MD
LG