Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Murrar Tsuntsaye ta kashe mutum a Ikko Najeria


Idan baku manta ba, a ruhotannin da muke gabatar maku kowa ne mako cikin shirye-shiryenmu galibi da safe, mun bada labarin sake bullar cutar masassarar Tsuntsaye a Nigeria. Farko ta bulla ne a jihar Kano, kana daga bisani lamarin ya bazu ya zuwa jihohi 22. Bullar cutar a jikin dan adam ta faru ne a Lagos, inda wata ‘yar shekara 22 daga cikin iyalan Mr. Chukwuma Nwanze ta rasu a unguwar Oke-Afar kusa da gundumar Solo.

Mahukuntan Nigeria ne suka tabbatar da hakan sakamakon wasu binciken da aka gudanar a gida da wajen Nigeria. Alamun Cutar a Dan Adam Tana fara wa ne da Mura. Bayan kwana daya zuwa biyu, sai Zazzabi mai zafi, daga nan sai mutum ya kasa nufashi, in da karar kwana mutun sai ya mutu. Galibi in dai har ita ce, bata wuce Kwana uku sai mutuwa. Dr. Abdulsalam Nasidi, darektan kula da cutukan dake addabar bil-adama na ma'aikatar kiwon lafiya ta tarayyar Nigeria ne ya bayyana hakan. Ya kuma shawarci mutane da su lura, da zarar mura ta rikide zuwa zazzabi, to a hamzarta zuwa babban asibiti mafi kusa, dan a samu magunguna da bincike na kimiya. A cewarsa, an rarraba maganin kashe kwayoyin ita wannan cutar a manyan asibitocin na jihohin da Murar Tsuntsaye ta bulla a bana.

RIGAKAFI 1. Babban rigakafin kamu wa da cutar murar tsuntsaye ya hada da fesa ruwan magani a hannu, da kafafuwa da kuma tayoyin mota kafin a shiga gonar kiwon Kaji, haka kuma za a sake yi idan za a fita daga gonar.

2. kada mutun yaci naman kazar da bata da lafiya don gudun cin wacce ta harbu da cutar murar tsuntsaye.

3. Idan an ga kaji da yawa sun mutun lokaci daya, to babban alamar bullar cutar ke nan a gida ko gonar da ake kiwon kaji. Sai a hamzarta a sanar da ma’aikatar Gona, data Lafiya dan a kashe kajin dake gonar, a kona gawarsu, sa’annan a binne tokar.

4. Jama su sanar da hukuma idan an ga miyagun mutane suna gwanjon kaji, domin wasu don gudun hasara, sai su ruga kasuwanni kauye ko birane suna gwanjon kajin da aka dauko daga gonakin da suka harbu da cutar murar tsuntsaye.,

5. Duk wanda zai ci naman kaji ko na tsuntsaye, ya tabbatar da sun dahu sosai, in kuma na gashi ne, to a gasa su sosai in kuma na suya ne, a soyasu rumui. 6. An kuma hana shan danyen kwai yanzu saboda wannan muguwar cutar.

A kuma soya kwai ya soyu kayau, ba irin suyar nasara ba wato half-done na rabi-da-rabi. Likitocin sun ce hakan na kasadar yada cutar ta shafi dan adam. Wanan tambihin, mun same shi ne daga

Dr. Nasidi, a hirar da suka yi da wakilinmu na Abuja, Sani malumfashi. ALBISHIR GA MASU KIWON KAJI Gwamnatin Tarayyar Nigeria, ta ware kudi yanzu don biyan kudin kazar da aka kasha da daraja ba itrin yadda ta biya ba a bara. Yin hakan ya biyo bayan yadda mutane basu son sanar da hukuma irin barnar da cutar tayi wa kajin gonakinsu. Saboda haka ya ku jama’a sai ayi hattara ba haushe yace da muguwar raya, gwamma kin tashi.

XS
SM
MD
LG