Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan sa kai na yankin Neja Delta sun saki ma’aikatan jirgin Ruwan nan ‘yan kasar Phillipins


Jami’an gwamnatin Nigeria sunce mayakan sa kai na yankin Neja Delta sun saki ma’aikatan jirgin Ruwan nan ‘yan kasar Phillipins su 24 da suka kama suna garkuwa dasu. A ranar 20 ga watan jiya ne aka sace ma’aikatan daga cikin wani jirgin Ruwan daukar kaya na kasar jamus daya yada zango a birnin Wari dake kudu maso yammacin Nigeria.

Kakakin gwamantin jahar Delta Sheddy Ozoene yace ma’aikatan ‘yan kasar Philipins sun koma cikin jirgin daukar kayan kuma sun kama kama hanya zuwa bakin gaba a garin Wari. Kamfanin dillancin labaru na Ruwaitsa ya ce an sako ma’aikatan ne saboda tausayi da nuna jin kai kawai ba tare da an baiwa mayakan sa kan wani kudi ba.

A yankin Neja Delta dai mayakan sa kai suna ci gaba da kame kamen ma’aikatan kamfanonin mai suna tsaresu. ‘yan tawayen sunce suna son gwamantin Nigeria ta rika baiwa ‘yankin nasu kaso mai tsoka daga cikin cinikin da tayi na Manfetur da take tatsa daga yankinsu.

XS
SM
MD
LG