Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Sun Salwanta A Hadarin Jirgin Saman Indonisia


Jirgin saman fasinja na kamfanin Garuda, kirar Boeing 737 dauke da fasinjoji 133 da ma’aikatan jirgin, ya kama wuta bayan saukarasa a tashar jiragen saman Yogyakarata, da sanyin safiyar Laraba. Daga saukar jirgin, sai ya kasa tsayawa, ya zarce cikin wata gonar shinkafa. Mai magana da yawun fada shugaban kasar Indonesia, Dino Djalil, yace shugaba Susilo Bambang Yudhyono ya bada umarni ayi cikakken binciken musabbabin wannan hadari, na biyu a kasar cikin watanni biyu. Yace Ya bada umarni binciken dalilan da suka kawo wannan hadari. Kuma binciken zai duba dukkan al’amuran dake da nasaba da hadarin, daga kan matsalar inji, zuwa ta sakaci ko kuskuren dan adam, ko kuma wadansu dalilai na dabam. Akwai a kalla mutanen kasar Australia guda goma a cikin jirgin, da kuma wadansu jami’an diplomasiyyar kasashen waje, da manema labarai dake dauko rahotannin ziyarar Ministan harkokin Wajen Australia, Alexander Downer zuwa kasar ta Indonesia. An tabbatar cewa shi Downer baya cikin jirgin. Ana jinyar wadansu daga cikin wadanda hadarin ya rutsa dasu a asibitocin kasar, kuma har yanzu ana neman wadansu da suka bata. Mulyiadi, shine Shugaban Asibitin Panti Rini, dake garin Yoghyakarta, ya kuma ce asibitinsa na jinyar wasu daga cikin wadanda suka jikkata. Yace yawancinsu sun sami munanan raunukan kuna, da ‘yan kalilan kuma da suka sami yanka da ka karcewa daga baraguzan jirgin. Wani mutum mai suna Suarjono, wanda Allah ya ceta daga hadarin, ya shaidawa wata gidan talbijin na kasar Indonesia cewa yanayi garin garau yake lokacin da suka zo sauka, amma koda jirgin ya yiwo kasa, sai kawai suka ji ana ta girgiza shi. Yace jirgin dira yayi a kan kwalta, maimakon sauka, daga nan kuma sai ya kama wuta. Sauran fasinjojin jirgin sunce suna ta jin kauri tun kafin jirgin ma ya sauka.
XS
SM
MD
LG