Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sami Bullar Mashassharan Tsuntsaye a kasar Burma


Jaridar kasar Burma mallakar gwamnati ta tabbatar da cewa an sami bullar nau’in cutar murran tsuntsaye na H5N1 a garuruwa biyu na kasar. Jaridar New Light ta Myanmar tace a watan jiya ne aka samo samfurin nau’in cutar a wata gonar kiwon kayi da garuruwan Myangon da kuma Hlinethaya.

Kuma tunin tace an kona gonakin baki daya sannan aka bi aka fesa maganin kwari wanda zai iya kashe kwayoyin cutar. A wani labari mai kama da wannan kuma, jaridar tace cibiyar rayar da kasa da kasa ta Amirka ta samarwa kasar Burma agajin kayakin aiki na kudi dala dubu dari shida domin ta yi aikin rigakafin cutar mashassharan tsuntsaye.

XS
SM
MD
LG