Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Majalisar Ministocin Hadin Kai Ta Falasdinawa Ta Yi Zamanta Na Farko


Majalisar zartaswar sabuwar gwamnatin hadin kai ta Falasdinawa ta yi zamanta na farko, kwana guda a bayan da aka rantsar da ita.

Ministocin wannan gwamnatin karo-karo sun hallara jiya lahadi a birnin Gaza.

Ministan harkokin wajen Falasdinawa, Ziad Abu Amr, yayi kira ga bani Isra'ila da ta hada kai da sabuwar gwamnatin. Ya fada wa gidan rediyon Isra'ila cewa Hamas ta yarda zata mutunta yarjejeniyoyin cimma zaman lafiya wadanda suka yi na'am da kasancewar Isra'ila a zaman kasa.

Amma kuma majalisar zartaswar bani Isra'ila ta ki yarda da sabuwar gwamnatin ta Falasdinawa wadda ta kunshi Hamas da Fatah mai sassaucin ra'ayi. Firayim ministan Isra'ila, Ehud Olmert, ya fada jiya lahadi cewa akwai matsala game da gafakar sabuwar gwamnatin, a saboda ta yi kiran da a yi gwagwarmaya (da mamayar Isra'ila a yankin Falasdinawa) sannan kuma ta ki yarda da diyaucin Isra'ila.

Mr. Olmert ya ce ba za a yi tattaunawar neman zaman lafiya da sabuwar gwamnatin ba, amma zai ci gaba da tuntubar shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas na kungiyar Fatah mai sassaucin ra'ayi.

daftarin akidar Hamas yayi kiran da a shafe Isra'ila daga doron kasa.

XS
SM
MD
LG