Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani dan shekaru 21 da haifuwa ya Mutu a kasar Indonesia


Wani mutun dan kasar Indonesia ya rasa ransa a sakamakon cutar mashassharan Tsuntsaye. Mutuwan wannan mutun ya kara yawan adadin zuwa mutun 66. Jami’in Ma’aikatar lafiyar kasar Nyoman kandun yace mutumi na baya bana nan da ya mutun dan shekaru 21 da haifuwa ne.

kuma ya mutu a Asibit a gabashin lardin Java a garin Surabaya. Sabbin Labarai dake fito daga yankin sunce jami’a a kasar Thailand sun tabbatar cewa an sami bullar sabbin cutar murran tsuntsaye tsakanin kaji da wadansu tsuntsaye a wani lardi dake Arewa maso gabashin kasar, wannan shine karo na hudu da bullar cutar.

Likitocin Dabbobin kasar sunce gwajin da akayi a cibiyoyin nazarin murrar tsuntsaye sun tabbatar a ranar Lahade waccan cewa, tsuntsayen sun harbu da nau’in kwayar cutar ta H5N1 a wata gona dake lardin Mukdahan. Cutar Mashassharan tsuntsaye ta kashe mutane 17 a kasar Thailand tun daga lokacin da ta sake bullar a yankin Asia a shekara ta dubu biyu da 3. Ya zuwa wannan lokaci ta kashe mutane 170 a duk fadin duniya.

XS
SM
MD
LG