Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"yan Tawayen kasar Somalia sun kashe sojojin Ethopia


Shaidun gani da ido sunce ‘yan gwagwarmaya sun kashe sojojin Habasha, suka kuma rika jan gawawwakin biyu daga cikinsu a titunan birnin Mogadishu, bayan wata arangama mai tsanani tsakaninsu, wadda tayi sanadiyyar rasuwar a kalla mutane goma sha daya.

Wannan bata kashin ya faru ne a yau Laraba, bayan ‘yan gwagwarmayar sun kai farmaki kan wasu motoci masu sulke na sojin Habasha, dake sintiri a wata unguwa da ‘yan gwagwarmayar suka yi dandazo, a nan kudancin birnin Mogadishu. Sojojin na Habasha sun maida martani da manyan bindigogi, kuma sun raunata mutane da dama.

Wadanda suka ganewa idanunsu abin da ya faru sunce a kalla sojojin Habasha shida ne suka mutu. A watan Disamban bara Habasha ta tura sojojinta kasar Somaliya, inda ta taimakawa gwamnatin rikon kwarya suka kori masu kishin Islama, da ragamar yawancin kasar ke hannunsu a wancan lokaci.

XS
SM
MD
LG