Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

shugabannin kasashen kudancin Afirka zasu yi taro laraba domin....


Ministan harkokin wajen kasar Tanzania, yace shugabannin kasashen kudancin Afirka zasu taru a gobe laraba a babban birnin kasar Daresalam domin fara taron koli na kwanaki biyu don su tattauna rikicin siyasar kasar Zimbabwe. Shugaban kasar Tanzania, jakaya Kikwete shi zai jagoranci taron kolin shugabanni kasashen kudancin Afirka 14 na cikin kungiyar rayarwa ta kasshen kudancin Afirka.

Duk da haka kungiyar bata bada ajandar taron ba, to amma jami’an kasar Tanzaniya sunce zasu gayyaci kasar Zimbabwe a taron. Jaridar gwamnatin kasar Zimbabwe mai suna Herald ta ce shugaban kasar wanda ruwan rikicin siyasa ya cinye, Rober Mugabe zai je taron.

XS
SM
MD
LG