Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran ta saki sojojin Ruwan Birtaniya da ta kama


Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinnejad yayi ahuwa ga mayakan Ruwan Birtaniya su 15 wadanda jami’an tsaron kasar suka kama suka tsare tun cikin makonni biyu da suka wuce. Shugaba Ahmadi Nejad ya fadawa taron manema alabarai a birnin Tehran yau Laraba cewa yayiwa mayakan ruwa Birtaniya Ahuwa ne a amatsayin alfarma ko wata kyauta ga al’ummar Birtaniya baki daya.

Jami’an Kasar Parisan sunce a gobe Alhamis ne zasu fice daga kasar. A birnin London kuma PM Birtaniya, Tony Blair ya fadawa manema labarai cewa Birtaniya batada haushi akan al’umman kasar Iran, kuma yayi fatar warware rikici tsakanin Birtaniya da Iran ta hanyar lumana.

Tony Blair yace “Ina farin ciki cewa Mr Ahamadi Nejada ya fada cikin wata wasika cewa Birtaniya ta yi alkawari ba zata sake shiga ruwan kasar Iran nan gaba ba, Iran tace mayakan ruwan birtaniya su 15 an kama su ne a yankin ruwan Iran, wadannan bayanai duk Birtaniya ta musanta su”.

XS
SM
MD
LG