Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu zanga-zangar sun hallara a birnin Najaf dake kudancin kasar domin yin juyayin ragayowar shekara ta hudu da hambare gawamnatin saddan Husaini


Masu zanga-zangar sun hallara a birnin Najaf dake kudancin kasar domin yin juyayin ragayowar shekara ta hudu da hambare gawamnatin saddan Husaini da sojojin kawance sukayi a Bagadaza. Daruruwan su sunyi jerin gwano daga birnin Kufa har zuwa garin Najaf yawancin su sunje cikin motocin safar daga birane dabam daban harma da birnin Bagadaza.

An dauki tsauraran matakan tsaro inda‘yansandan da sojojin Iraq suke gadin bakin iyakar shiga gari. A duk fadin kasar kuma dokar da mahukuntan kasar suka kafa ta hana sintirin motoci a yau ta fara aiki tun daga farfe 5 na safiyar yau Litinin a gogon kasar. Har zuwa tsakiyar ba’aga malamin man matashi Mutada Al Sadr ya fito yayi jawabi a dandalin gangamin ba.

Jami’an Amirka sunce Muktada Alsadr ya je kasar Iran ya buya domin ya gujewa hare haren ba sani ba sabo da sukeyi kwanan nan domin fatattakar ‘yan gwagwarmaya, to amma mukarrabansa sun musanta wannan ikirari suna masu cewa Malamin yana cikin kasar baije ko ina ba.

XS
SM
MD
LG