Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya mai barin gado, Chief Olusegun Obasanjo, ya bukaci kasashen duniya da su dan tsahirtawa Najeriya


Shugaban Najeriya mai barin gado, Chief Olusegun Obasanjo, ya bukaci kasashen duniya da su dan tsahirtawa Najeriya, a kokarin da take yi na gudanar da zaben shugaban kasa a gobe. A jawabin da yayi wa al’ummar kasar a yau Juma’a, shugaba Obasanjo ya tabo batun magudi da aka ce ya zama ruwan dare a zabukan da aka gudaar a satin da ya wuce.

Yace hakika, ba a rasa ‘yan kura kurai a zaben, amma yace ya kamata a fahimci matsayin jaririyar dimokradiyyar kasar. “Kamata yayi mu maida kai wajen gyara kura kuran da aka yi, maimakon a fasa kowa ya rasa” inji Obasanjo. A halin da ake ciki kuma, a yayin da ake shirye shiryen gudanar da Zaben Shugaban Kasa na na Majalisun Taraiya a gobe, wasu kanan jam’iyyu a kasar sunce sudai basu ga amfanin shiga zabukan ba, dak da cewa manyan jam’iyyun adawa sun yanke shawarar shiga. Wakilin Muryar Amurka Nico Colombant yayi tattaki zuwa Zariya, a arewacin najeriya, inda yayi kacibus da Alhaji Sani Sha’aban, Dan Takarar Gwamna da aka kayar a zaben da ya gabata, yana tattaunawa da manema labarai. Ya jaddada zargin magudi a zabe, inda har ma yace tun ma kafin a fara zaben, aka riga aka makare wasu akwatunan da kuri’un da aka kadawa jam’iyyar PDP. Ya kuma koka da yadda sojoji da ‘yan sanda suka kakkafa shingaye a sassan kasar, da dokar hana watayawa da aka sassaka a jihohin kasar.

Tsohon shugaban mulkin saja a kasar, Janar Muhammadu Buhari, wanda ke takara a karkashin jam’iyyar adawa mafi karfi, yana da matukar farin jini a Arewa. Amma daga yanki daya suka fito da Alhaji Umaru Musa ‘Yar Aduwa, dan takarar jam’iyya mai mulki. A goben dai za kuma a zabi ‘yan Majalisun Taraiya. Babban abin da ‘yan Najeriya zasu fi tuna majalisu masu barin gado dashi, shine yadda suka murkushe yunkurin tazarce da wasu magoya bayan Obasanjo suka yi kokarin dabbakawa.

XS
SM
MD
LG