Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Lebanon an kashe mutane biyar, dukkansu fararen hula ‘yan palesdinu, yayinda aka shiga rana ta biyu da gwabcewar


Ma’aikatan assibitocin Lebanon sunce an kashe mutane biyar, dukkansu fararen hula ‘yan palesdinu, yayinda aka shiga rana ta biyu da gwabcewar kazamar bata-kashi tsakanin sojojin Lebanon da mayakan Islama a wani sansanin ‘yan gudun hijira na Palesdinawa.

A yau Litinin ne sojan na Lebanon suka ci gaba da fattatakar wadannan mayakan na wata kungiyar da ake kira Fath-al-Islam dake a wannan sansanin na Nahr-el-Bared dake birnin Tripoli na arewancin Lebanon din.

Jami’ai sunce ko a jiya Lahadi ma mutane kusan 50 aka hallaka, ciki harda sojoji 27 da kuma mayakan Islama din su 17, tareda wasu fararen hula. Daya daga cikin wadanda aka kashen shine wani dan kishin Islama da aka zarge shi da yunkurin (da ya ci tura) na tarwatsa wasu jiragen kasa a bara a Jamus, ana kiransa Saddam el-Hajdib, wanda aka ga gawarsa tareda da gawawakin wasu ‘yan kungiyar Fatah-al-Islam su 10 a cikin wani gidan da sojan Lebanon din suka yi wa kaca-kaca.

Duk wannan fadan dai ya barke ne bayanda ‘yansanda suka kai farmaki a wata unguwa ta Tripoli inda suka je neman irin wadannan mayakan na ‘yan kishin Islam din. 2

XS
SM
MD
LG