Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Zata Sake Fasalin Darussan Addinin Musulunci A Jami’o’in Kasar


Prime Ministan Birtaniya mai barin gado, Mr. Tony Blair ya baiyana wani shiri na horas da malaman addinin musulunci a jami’o’in kasar, da nufin yada addinin Islama mai sassauci. A jiya Mr. Blair ya baiyana wannan shiri, a wajen wani taron bita a kan addinin musulunci da aka gudanar a birnin London.

Yace yana tsoron masu tsattsauran ra’ayi zasu iya dusashe amon abin da yake ganin shine musulunci na hakika. Wannan shiri da ake sa ran zai ci kimanin dala miliyan biyu, ya biyo bayan rahoton wani bincike ne, wanda ya nuna cewa nazarin addinin musulunci a birtaniya, yana dogara ne kacokan a kan yanayin rayuwar Gabas ta Tsakiya, inda akan yi watsi da rayuwar musulmin Birtaniya.

Mr. Blair ya kara jaddada cewa shawararsa ta marawa Amurka baya a yakin Afghanistan da Iraqi, bata da wata alaka da addini.

XS
SM
MD
LG