Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Da Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka Sun Cimma Yarjejeniya Kan Darfur


Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka, KTKA, sun cimma yarjejeniya a kan shirin girka rundunar kiyaye zaman lafiya mai sojoji dubu 23 a yankin Darfur na kasar Sudan.

Wannan shirin ya tanadi raba ikon gudanar da rundunar a tsakanin sassan biyu, amma kuma bai bayyana yadda hakan zai yi aiki ba. Jami’an diflomasiyya suka ce Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka zata rike ikon gudanar da ayyukan yau da kullum na rundunar hadin guiwar, yayin da ikon ayyukan rundunar baki daya zai kasance a hannun MDD.

Sai dai kuma, mataimakin sakataren MDD mai kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya, Hedi Annabi, ya ce za a fuskanci wahala wajen aiwatar da wannan shirin, yana mai cewa, "...wannan sabon kauli ne a gare mu. ba mu taba gudanar da ayyukan rundunar hadin guiwa ba. Duk wani kwararre kan ayyukan soja zai fada maka cewa duk wata rundunar da take da masu yin iko da ita da yawa, to zata fuskanci wahalar gudanarwa a saboda tilas sai dukkan sassan sun yarda da inda za a dosa."

Kafin a fara aiki da wannan shirin, tilas sai gwamnatin kasar Sudan ta amince da shi. A can baya dai, gwamnatin ta Sudan ta ki yarda da tura sojojin MDD masu yawa zuwa Darfur, ta kuma ce tilas duk wata rundunar kiyaye zaman lafiyar da za a tura ta kasance karkashin ikon kasashen Afirka.

XS
SM
MD
LG