Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai kamfanin hakar gawayin Coal a Jihar Utah a Amurka ya ce zai dauki akalla kwana uku kamin masu ceton rai su kai inda ma’aikatan su ke


Wani mai kamfanin hakar gawayin Coal a Jihar Utah dake arewacin Amurka ya ce zai dauki akalla kwanaki uku kamin masu ceton rai su kai inda ma’aikatan hakar gawayi su shida suka makale sakamakon toshewar hanyar fita,can karkashin kasa fiye da zurfin mita 450.

Robert Murray,na kamfanin hakar gwayi da ake kira Crandall Canyon Mine, ya fada jiya Talata cewa babu tabbas ya’Allah ma’aikatan suna da rai ko a’a.Amma ya ce idan har suna da rai suna da isashen ruwa da iskar shaka da zasu wadace su har sai zuwa lokacinda masu ceto zasu kai ga inda suke.

Haka kuma Murray ya da ge cewa ramin hakar gawayin ya burma ne sakamakon girgizar kasa,amma masana kimiyyar kasa, sunce sikelin motsin kasa,ya auna burmewar ramin hakar gwayin ne,ba girgizar kasa kasa ba.Ba dai wanda yayi magana da wadanan ma’aikatan tun shekaranjiya Litinin, ranar da ramen ya tuzga a kansu. Yanzu haka ana sa ran cewa tsakanin ma’aikatan da abin ya rutsa da su da kuma masu kokarin ceto su, akwai tazarar fiyeda mita 500.

XS
SM
MD
LG