Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Taleban Sun Sako 'Yan Kasar Koriya Ta Kudu Su 12


’Yan gwagwarmayar Taleban sun sako ’yan kasar Koriya ta Kudu su 12 daga cikin 19 da suka sace kusan makonni shida da suka wuce.

’Yan Taleban sun sako mutanen a wasu wurare dabam-dabam har uku a yau laraba, suka mika su ga shugabannin kabilun lardin Ghazni na kudancin kasar. Daga nan aka damka ’yan Koriya ta Kudun a hannun jami’an kungiyar agaji ta Red Cross.

Jiya talata, Taleban ta ce nan bada jimawa ba zata sako dukkan mutanen da take yin garkuwa da su. Wannan sanarwa ta biyo bayan tattaunawar gaba da gaba da mashawartan KOriya ta Kudu wadanda suka yarda zasu janye 200 daga cikin sojojin kasar dake Afghanistan nan da karshen shekara, zasu kuma dakatar da ayyukan mishan a kasar.

’Yan siyasar Afghanistan da dama sun soki wannan yarjejeniya suna amsu fadin cewa zata karfafa guiwar sace mutane nan gaba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Tom Casey, yayi marhabin da sako mutanen da aka yi garkuwa da su. Haka kuma, yayi watsi da ikirarin cewar yarjejeniyar da Koriya ta Kudu ta kulla da Taleban zata bayar da halalcin siyasa ga kungiyar.

XS
SM
MD
LG