Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Su Na Yin Zanga-Zanga A Garin Jena A Jihar Louisiana


Dubban 'yan zanga-zanga daga ko ina a nan Amurka sun hallara a wani dan karamin gari dake Jihar Louisiana a kudancin wannan kasa, domin janyo hankali ga abinda suka kira bambancin launin fata da ake nuna ma wasu dalibai bakaken fata da suka yi fada da wani saurayi bature a wata makarantar sakandaren garin.

Sanannun shugabannin kare hakkin jinsuna tsiraru na Amurka da suka yi jawabi gaban wannan gangami a garin Jena, su na kwatanta zanga-zangar da irin wadda aka yi ta yi ta neman hakkin bakake a shekarun 1960.

A bayan da aka yi wata da watanni ana zaman doya da manja na bambancin launin fata a wannan makaranta, an gurfanar da dalibai shida bakaken fata a gaban kotu ana tuhumarsu da laifin kokarin kisan kai a saboda sun doki wani dalibi bature.

Daga baya an rage tsananin laifuffukan da ake tuhumar hudu daga cikin bakaken fatar da aikatawa, yayin da a makon jiya wata kotun daukaka kara ta soke hukumcin daurin shekaru 15 da aka yanke a kan bakar fata na biyar.

Amma shugabannin 'yan rajin kare hakkin tsirarun jinsuna sun ce irin wannan dabi'a da aka nuna ma daliban bakake, ta nuna cewa har yanzu akwai sauran wariyar launin fata a jihohin da suke kudancin wannan kasa, da kuma a kotuna.

A lokacin da aka tambaye shi game da wannan lamari a yau alhamis, shugaba Bush ya ce yana mai bakin cikinsa. Ya ce hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya, FBI, da kuma ma'aikatar shari'a su na sanya idanu a kan abubuwan dake faruwa.

Wasu mazauna garin Jena mai mutane dubu uku da dari biyar sun ce a lokuta da dama garin, wanda akasarin mutanensa turawa ne, yana fuskantar matsalar bambancin launin fata. Suka ce dukar da aka yi ma dalibi baturen na da asali daga wani lamarin tun watan Agustar bara a lokacin da wani dalibi bakar fata ya nuna sha'awar zama a inuwar wata bishiyar da dalibai suka mayar tamkar tasu ce kawai.

A bayan da wannan dalibi bakar fata ya nuna sha’awar zama a inuwar wannan bishiya, sai dalibai turawa suka daura igiyoyi na rataye mutane a jiki, matakin dake tuna ma bakar fata yadda haka siddan turawa suka yi ta rataye su a nan Amurka a farko-farkon karnin da ya shige.

XS
SM
MD
LG