Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Umar Yar’adua na Najeriya ya ce Gwamnatinsa za ta aiwatar da dukkan shawarwari da kwamitin da ya kafa ya sake nazarin matsalar zabe a najeriya


Shugaba Umar Yar’adua na Najeriya ya ce Gwamnatinsa za ta aiwatar da dukkan shawarwari da kwamitin da ya kafa ya sake nazarin matsalar zabe a najeriya ya gabatar masa a karkashin jagorancin Masanin Shari’a Mamman Lawal Uwais.

.

Shugaban wanda ya fadi haka a hirar da ya yi da Muriyar Amurka lokacin da ya kawo ziyara Amurka domin halartar babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya na sittin biyu a birnin New York,ya yabawa Gwamnatin da ta shude ganin a bana kungiyar yaki da cin hanci a hukumomi na kasashen Duniya watau Transparency International,ta baiwa Najeriya rukuni na 32,maimakon matsayinta na kasashen karshe da suka shahara wajen cin hanci da rashawa a Duniya baki daya.

Da yake amsa tambaya gameda umurni da gwamnatinsa ta bayar kan yadda Hukumar EFCC za ta nemi izinin Atoni Janar na Najeriya kamin ta gurfanadda wadanda take tuhuma,shugaban yace wannan ba haka yake ba,yace EFCC da takwarorin ta za su ci gaba da gudanar da ayyukan su kamar yadda suka saba.Amma idan Atoni Janar ya lura cewa suna kauce hanya yana da iko kamar yadda tsarin Mulki ya bashi ya tsaida karar,koma ya karbe ta baki daya. Yayi alkwarin Gwamnatin sa ba za ta ba sani ba sabo wajen yaki da cin hanci da rashawa har sai kasar ta tsabta ce baki daya

Shugaba Umar ‘Yar’adua,a hirar ya sa ke nanata kira da ya yi a jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dinkin Duniya na bukatar ayi garambawul ga kwamitin sulhu domin a baiwa Afirka kujera ta din din din.

.

XS
SM
MD
LG