Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Litinin ne Ma’aikatar tsaro ta Amurka zata fara gundanar  da sabon ofishin runduna da Amurka ta kafa


Yau Litinin ne Ma’aikatar tsaro ta Amurka zata fara gundanar da sabon ofishin runduna da Amurka ta kafa mai lura da shiyyar Afirka. Sabuwar rundunar sunan ta AFRICOM.

Rundunar sojojin Amurka tace sabuwar rundunar zata taimaka wajen raba kayan agaji da horaswa a nahiyar,da kuma lura da matakan yaki da ta’addanci.Kasashen Afirka da dama suna adawa sabuwar rundunar.Sunce Ma’aikatar tsaron bata bada bayanin sabuwar rundunar wacce aka karkasa tsakanin wasu rundunonin Amurka uku masu lura da wasu yankuna.

Wasu masu sukar lamirin sabon shirin kamar Afirka ta kudu sun bayyana fargabar amfani da rundunar wajen kara katsa lanadan da kuma amfani da karfin soja wajen kutsa kai cikin harkokin kasashe dake nahiyar.’Yan kasar Afrika da dama sun bayyana damuwar canjin zai fadada kasancewar Amurka a nahiyar.Amma Amurka ta ce ba zata gina sabbin sansanoni sojojin na ta a nahiyar.

XS
SM
MD
LG