Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PM Somaliya Ali Mohammed Gedi yayi murabus


PM Somaliya Ali Mohammed Gedi yayi murabus,bayan wani dogon zaman doya da manja tsakaninsa da shugaba kansa Abdullahi Yusuf,rashin jituwar da ta raba kawuna cikin Gwamnati rikon kwariyar kasar.

Mr. Gedi ya bada sanarwar murabus dinsa a jawabi da yayiwa wakilan Majalisa yau Litinin,a garin Baidoa dake kudu maso tsakiyar kasar. Yace zai ci gaba da aiki da wakilan Majalisa bisa kokarin dai daita al’amura cikin kasar. A jawabinsda ga Majalisa shima,shugaba Abudllahi Yusuf, ya murna da murabus din PM,yace zai tutubi wakilan Majalisa kamin ya zabi wadda zai gaji PM.

A makonni baya bayan nan,Mr. Yusuf yayi kokarin neman a jefa kuri’ar rashin amincewa shgabancin Mr. Gedi,wadda ya ke zargi da laifin kasa kawo karshen gwagwarmayar masu kishin Islama cikin fadar kasar Mugadishu,da kuma gazawarsa PM na rubuta sabon tsarin mulki.

Dukkan su biyu sun fito ne daga kabilu daban daban kishiyoyi. Daruruwan mutane ne suka arce daga birnin Mugadishu a ayau a loakcinda aka bada labarin jin karar manyan bindigogi da kanana ko ina cikin birnin.

XS
SM
MD
LG