Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Crsitina Fernandez de Kirchner, ta zama mace ta farko da aka taba zaba shugabar kasar Argentina


Crsitina Fernandez de Kirchner, ta zama mace ta farko da aka taba zaba shugabar kasar Argentina,da sakamakon zabe da aka yi jiya lahadi yana nunin ta sami kuri’u da ya rubanya na abokanan hamayya biyu da suke biye da ita.

Bayan an kidaya kamar kashi 94 cikin dari na kuri’a da aka kada a zaben na jiya, Ms Fernandez uwar gidan shugaban Argentina Nestor Kirchner, ta sami kashi 45 a zaben da yan takara 13 suka tsaya zabe. Abokanan takarar ta da suka kimanta, tsohon Ministan Tattalain arziki Roberto Lavagna,da kuma tsohuwar ‘yar Majalisa Elisa Carrio, duk sun mika wuya.

Wakilin MA Michael Bowman yana birnin Buenos Aires,inda Cristina Fernenadez de Kirchner zata karbi sandar Mulki daga hanun mijinta shugaban kasa Nestor Kirchner.

XS
SM
MD
LG