Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaron Paksitan sunyi amfani da borkono mai sa hawaye da kulakai a kokarin tarwatsa lauyoyi wadanda suke zanga zanga


Jami’an Tsaron Paksitan sunyi amfani da borkono mai sa hawaye da kulakai a kokarin tarwatsa lauyoyi wadanda suke zanga zanga a yau litinin domin adawa da dokar ta baci da shugaba Pervez Musharraf ya kafa.Anyi Zanga zanga mafi girma a birnin Lahore dake gabashin kasar,inda fiyeda lauyoyi dubu daya ne suka hallara a harabar kotun kasar suna ihu cewa, “katafi Musharraf,”Musharraf katafi!!!!.Haka kuma ‘yansanda sun kai hari har suka kama daruruwan masu zanga zanga a Karaci da Rawalpindi.

Gwamnatin Pakistan ta musanta rade rade cewa anyiwa Janar Musharraf daurin talala. Jami’ai sukace yana fadar gwamnati inda yake ganawa da jakadun kasashen ketare, domin yayi musu bayani kan dalilanda suka sanya ya dauki matakan kafa dokar ta baci cikin kasar ranar Asabar. Mr. Musharraf yace ya dauki matakan ne domin yin maganin mutane masu tsananin ra’ayi,da Alkalai da iko ya ratsa..

Amma masu sukar lamiri sunce yayi hakane kurum domin hana alkalan yanke hukunci gameda haliccin sake tsyawa takarar zabe da yayi cikin watan jiya,a yayinda yake ci gaba da rike mukamin babban hafsan sojin kasar. ‘Yansanda sun kama daruruwan lauyoyi ‘yan gwagwarmaya,da shugabannin ‘yan adawa tun ranar Asabar.Kuma an haramtawa kafofin yada labaru masu zaman kansu aiki.

XS
SM
MD
LG