Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata kotu a birnin Ndjamenan Chadi tace a ci gaba da rike ma’aikatan kungiyar nan ta Zoe’s Ark


Wata kotu a birnin Ndjamenan Chadi tace a ci gaba da rike ma’aikatan kungiyar nan ta Zoe’s Ark su shida, wadanda ake zargi da kokarin sace wasu yara fiye da 100, ‘yan kasar Chadi. A yau laraba kotun ta zauna, kuma tace a ci gaba ra rikesu a gidan wakafi har sai ta waiwayesu. Kotun ta nyanke wannan hukunci ne kuwa duk da korafin da kasar farnsa ke yi a kan yanayin shari’ar.

A wani labarin kuma, daruruwan mutane ne suka yi zanga zanga a titunan birnin Ndjamena, don nuna fushinsu ga kokarin sace yara da kungiyar ta Zoe’s Ark tayi. Masu zanga zangar sun je har ofishin jakadancin faransa, inda suka rika wadansu kalaman kin jinin Faransa, suka kuma rika jifan motocin dake dauke da baki ‘yan kasashen waje. Amma dai ‘yan sanda sunyi banga banga, suka bada tsaro ga ofishin jakadancin na Faransa.

A watan jiya ne gwamnatin kasar Chadi ta dakatar da wani jirgin sama dake shirin daukar yara dari da uku, kungiyar tace wai zata samawa iyayen rana a Faransa. Abin da ya bata lamarin ma, shine yadda wasu jami’an kungiyar suka ce yaran marayu ne daga yankin Darfur na kasar Sudan.

Amma kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun tabbatar da cewa yawancin yaran suna da a kalla daya daga cikin iyayensu a raye, kuma yawancinsu ‘yan kasar Chadi ne.

XS
SM
MD
LG