Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yana Shirin Ganawa Da Mahmoud Abbas Da Ehud Olmert


Shugaba Bush zai gana da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da firayim ministan bani Isra’ila Ehud Olmert nan gaba yau litinin a fadarsa ta White House, kafin taron da za a bude gobe talata na neman zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

Cikin wata sanarwar da ya bayar jiya lahadi, Mr. Bush ya ce manufofin wannan taro guda uku ne: kaddamar da yin shawarwari, bayar da dama ga ’yan bani Isra’ila da Falasdinawa su sake rungumar taswirar cimma zaman lafiya da kuma neman goyon bayan kasashen duniya ga kokarin gina cibiyoyin dimokuradiyya a Falasdinu.

Mai bayar da shawara kan harkokin tsaron kasa na Amurka ya ce taron zaman lafiya a gabas ta tsakiya da za a yi cikin wannan makon a nan Amurka zai bayar da wata irin dama ta tattaunawa, amma kuma ya jaddada cewa ba dandali ne na yin shawarwari ba. Stephen Hadley ya fadawa ’yan jarida jiya lahadi cewa taron da za a yi a birnin Annapolis wata dama ce ga ’yan bani Isra’ila da Falasdinawa su rungumi turba ta yin shawarwari. Stephen Hadley ya ce har yanzu ana kokarin kammala zana ajandar taron.

Jiya lahadi, kasar Sham ta ceta yanke shawarar halartar taron na gobe talata a saboda an kara batun zaman lafiya a tsakaninta da bani Isra’ila a cikin abubuwan da za a tattauna.

XS
SM
MD
LG