Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Alhamis Za A Rantsar Da Pervez Musharraf A Zaman Shugaban Farar Hula Na Kasar Pakistan


A yau alhamis za a rantsar da shugaban Pakistan Pervez Musharraf a zaman shugaban farar hula, abinda zai kawo karshen shekaru 46 da ya shafe a cikin rundunar sojojin kasar.

A bayan bukin rantsar da shi, Malam Musharraf zai yi jawabi ga al’ummar kasar ta cikin telebijin, inda manyan jami’ai suka ce watakila zai bayyana ranar dage dokar-ta-bacin da ya kafa ranar 3 ga watan Nuwamba.

Shugaba Musharraf, wanda ya sauka daga mukamin babban hafsan sojojin kasar, ya mika wannan kujera tasa jiya laraba a lokacin da ya mika sandar wannan mukami ga magajinsa, Janar Ashfaq Kayani a hedkwatar rundunar sojojin kasar dake birnin Rawalpindi. A cikin jawabin ban kwana da yayi idanunsa cike da kwalla, shugaba Musharraf ya ce yayi alfaharin jagorancin rundunar sojojin, wadda ya ce ita ce rayuwarsu har na tsawon shekaru kusan hamsin.

Shugabannin adawa da tsoffin firayim ministoci Benazir Bhutto da Nawaz Sharif duk sun yi marhabin da murabus din da shugaba Musharraf yayi daga rundunar sojojin kasar.

XS
SM
MD
LG