Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane hamsin da shida sun halaka a wani Jirgin jigilar Fasinja na Turkiyya


Wani Jirgin jigilar Fasinja na Turkiyya yayi hadari a kudu maso yammacin Kasar,kuma duka mutane 56 dake cikinsa sun halaka. Jami’an Hukumar zirga zirgan Jirage ta kasar tace masu aikin ceto sun isa inda jirgin ya fadi,kuma sun bada labarin cewa babu wadanda suka tsira.

Jirgin, na wani Kamfani mai zaman kansa da ake kira Atlas Jetliner, yana dauke da Fasinja 49,da ma’aikatan jirgin bakwai,yayi hadarin ne da safiyar yau Jumma’a a wani yanki mai tsaunuka kusa da birnin Isparta,jim kadan bayan da matukin jirgin ya bada sanarwar shirin sauka a filin saukar jiragen saman dake birnin.

Jami’ai sukace babu alamar lalacewa,kuma babu matsala da yanayi a ayankin. Hukumar lura da zirga zirgar jiragen sama ta Turkiyya tace ta gano na’urorin adana bayanai na jirgin wadanda za su taimaka wajen tantance musabbabin hadarin. Ma’aikatar tace jirgin ya fadi ne kilomita 11 da ga inda hanyar saukar jiragen take.

XS
SM
MD
LG