Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Taron Kolin Kasashen Duniya Kan Sauyin Yanayi A Bali


Jami'an gwamnati da 'yan rajin kare muhalli su fiye da dubu goma, daga kasashe dari da casa'in, sun bude wani taron kolin da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya kan sauyin yanayi a tsibirin Bali na kasar Indonesiya.

Manufar wannan taron kwanaki 12 da aka fara yau litinin ita ce kara kaimin yaki da yadda yanayin duniya ke kara yin zafi, tare da samo yarjejeniyar da zata maye gurbin Yarjejeniyar Kyoto ta yaki da dumin duniya wadda aikinta zai kare a 2012.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya kamata a fara tattauna yarjejeniyar da zata maye gurbin ta Kyoto nan da nan a kuma kammala ta nan da 2009 domin a samu magajiyar yarjejeniya kan lokaci kafin kare aikin ta Kyoton.

Shugaba Bush na Amurka yayi kiran da a dauki matakan shawo kan sauyin yanayi, amma kuma bisa ka'idojin da suka yi dabam da wadanda ke cikin Yarjejeniyar Kyoto, yarjejeniyar da Amurka ta ki yarda ta amince da ita balle ta aiwatar.

A 1997, Yarjejeniyar Kyoto ta bukaci kasashe 36 da suke da arzikin masana'antu su rage fitar da iskar gas mai kara dumama duniya, iskar da aka dora mata laifin karuwar zafi a duniya. An bukaci su yi hakan cikin shekaru 5 kama daga shekarar 2008.

XS
SM
MD
LG