Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kafa Sabon Takunkumi A Kan Jami'an Zimbabwe Masu Alaka Da Shugaba Robert Mugabe


Amurka ta kafa sabon takunkumi a kan jami'an Zimbabwe masu alaka da shugaba Robert Mugabe, mutumin da Amurka take zargi da mummunan keta hakkin bil Adama.

Mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da al'amuran Afirka, Jendayi Frazer, ita ce ta bayyana wadannan matakan jiya litinin. Matakan sun hada da takunkumin kudi da na tafiye-tafiye.

Frazer ta ce takunkumin tafiye-tafiyen zai shafi mutane 38, cikinsu har da jami'an tsaro na kasa na Zimbabwe da wasu balagaggun 'ya'yan jami'an gwamnatin Zimbabwe dake yin karatu a nan Amurka.

Jami'ar ta yi kashedin cewa Amurka tana iya kara daukar wasu matakan kuntatawar idan har aka ci gaba da keta hakkin bil Adama tare da tashin hankalin siyasa a kasar. ta kara da cewa hanya guda ta sauya akalar lamarin ita ce mayar da kasar Zimbabwe a kan turbar dimokuradiyya.

Amurka, da Tarayyar Turai da kuma Kungiyar Kwamanwels sun kafa takunkumi a kan kasar Zimbabwe, su na zargin Mr. Mugabe da laifin murkushe 'yancin dimokuradiyya da masu yin adawa da shi.

XS
SM
MD
LG