Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yace Har Yanzu Bashi Da Natsuwa A Kan Iran


Shugaba Bush na Amurka, ya nace kan cewa shi fa har yanzu yana da shakkunsa a kan Farisa, duk da wanketa da wani rahoton hukumomin Amurka yayi daga zargin kokarin kera makaman nukiliya. A wani bayani da yayi a Fadar White House yau talata, Shugaba Bush yace rahoton Hukumar Leken Asiri na cewa Iran ta dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya, wani hannunka mai sanda ne, cewa kasar zata iya dawowa da shirinta. Yace “Kasar tana da hadari fa. Iran tana da hadar.

Kuma Iran zata kasance babban hadari idan suka sami fasahar kera makaman nukiliya.” A yau Talata wani Babban Jami’in Hukumar kula da Makamashin Atom, yayi magana daga birnin Vienna, inda yace wannan rahoto ya tabbatar da gaskiyar kalamansu cewa supetocinsu basu sami wata hujja ba, da zasu zargi Iran na kokarin kera makaman nukiliya, kuma basu hango wani hadari ba.

Shi kuma Ministan Harkokin Wajen Iran, Manoucher Muttaki’i, da yake magana da wani gidan rediyon Iran, yace sabon rahoton na Hukumar Leken Asiri, ya kara karfafa matsayinsu, ya kuma tabbatar da maganarsu cewa shirin nukiliyarsu ba na tashin hankali bane. Yace “Iran tana maraba da kasashen da a yanzu suka amince su kalleta da sabuwar fuska.”

XS
SM
MD
LG