Nigeria ta soke kwangilar data baiwa kamfanin kayayyakin sadarwa na Jamus Siemens a yayinda take binciken zarge zargen cewa kamfanin Siemens ya baiwa wasu jami’an Nigeria cin hancin dala miliyan goma sha hudu. Mai magana da yawun gwamnatin Nigeria John Odey yace a jiya laraba aka soke kwangilar.
Yace gwamnati ba zata kara hulda da kamfanin Siemens a yayinda ake ci gaba da gudanar da bincike akan zarge zargen ya bada cin hanci ba. A watan oktoba wata kotu a kasar Jamus taci kamfanin Siemens tara dala miliyan maitan da arba’in da takwas a saboda ya baiwa wasu jami’an gwamnati a Nigeria da Russia da kuma Libya cin hanci domin a bashi kwangilar.
Shugaban Nigeria Umar Musa YarAdua yayi alkawarin cewa ba zai yarda da cin hanci da rashawa ba, kuma za’a hukunta duk wanda aka baiwa cin hanci.