Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa Na Nijeriya Ya Ce Shi Bai Ce Ya Yarda Amurka Ta Girka Sojojinta A Afirka Ba


Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa na Nijeriya yayi bayani a game da yarjejeniyar da ya cimma da shugaba Bush na Amurka dangane da hadin kan soja a tsakanin kasashensu biyu.

A cikin hira da Sashen Hausa na Muryar Amurka, shugaba 'Yar'aduwa ya ce ba kamar yadda kafofin labarai suka yi ta yadawa ba, shi bai ce ya yarda ya kyale Amurka ta kafa sansanin soja a Nijeriya a lokacin da suka gana da shugaba Bush ranar alhamis a nan Washington ba.

A maimakon haka, shugaba 'Yar'aduwa ya ce ya nemi tallafin rundunar sojojin Amurka mai kula da nahiyar Afirka, AFRICOM, wajen kafa wata rundunar sojoji ta kasashen Afirka zalla, wadda za a kafa sansanoninta a dukkan yankunan tarayyar tattalin arziki da ake da su a Afirka. Wannan runduna ta Afirka zata yi aikin kiyaye zaman lafiya ne a fadin nahiyar.

Shugaban na Nijeriya ya ce shi irin taimakon da ya nema daga rundunar ta AFRICOM ya hada da na makamai, kayan aiki da da kuma horaswar ad zasu taimaka ma sojojin na Afirka wajen gudanar da ayyukansu.

Haka kuma, shugaba 'Yar'aduwa yayi magana dangane da shirin gwamnatinsa mai ajanda bakwai da kokarin wanzar da zaman lafiya a yankin makwararin ruwan kogin Kwara, watau Niger Delta, inda akasarin arzikin man fetur na Nijeriya yake.

Domin jin wannan hira da shugaba 'Yar'aduwa sai a matsa rubutun dake saman wannan labari, don jin abinda ya ce game da rundunar ta kasashen Afirka da kuma ajandar gwamnatinsa.

XS
SM
MD
LG