Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyan gwamnatin kasar Afrika Ta Kudu ya ce ya na da isasshiyar shaidar shigar da karar cin hanci a kan Jacob Zuma


Babban lauyan gwamnatin kasar Afrika ta kudu ya ce ya na da isasshiyar shaidar shigar da karar cin hanci a kan Jacob Zuma, sabon shugaban jam’iyyar da ke mulki a kasar. Mokotedi Mpshe, shugaban rikon hukumar shigar da ƙara ta kasa baki ɗaya, ya yi wannan furuci ne alhamis ɗin nan a yayin wata tattaunawar da wani gidan rediyon Africa ta kudu ya yi da shi.

Ranar talata aka zabi Jacob Zuma a mukamin shugaban jam’iyyar ANC mai mulkin kasar, ya yi kakkarfar galabar da ba tantama akan shugaba Thabo Mbeki cikin wata munmunar takarar da akai jifan juna da maganganu masu ɗaci. A shekarar dubu biyu da biyar shugaba Mr.Mbeki ya yi waje da Zuma daga mukamin shi na mataimakin shugaban kasa bisa zargin cewa ya karbi cin hanci, mai nasaba da wani cinikin makaman da gwamnati ta yi a lokaci.

Karshen ta dai watsi aka yi da wadannan zarge-zarge. Jacob Zuma bai ce lummakaifa ba game da furucin Mokotedi Mpshe na cewa ya na da isasshiyar shaidar shigar da kara a kan shi.

XS
SM
MD
LG