Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afghanistan Ta Kori Wani Jami'in Diflomasiyyar Turai Da Wani Ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya


Afghanistan ta umurci wani jami’in Kungiyar Tarayyar Turai, KTT, da wani ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da su bar kasar, tana mai fadin cewa su na yin barazana ga tsaron kasar.

Wani kakakin gwamnati, ya fada jiya talata cewa an tsare mutanen biyu, daya dan Britaniya dayan kuma dan kasar Ireland, tare da wasu abokan aikinsu ’yan Afghanistan. Ana zarginsu da yin taro da kabilu da kungiyoyi dabam-dabam, watakila cikinsu har da ’yan Taliban.

Kakakin ya ce an ayyana ’yan kasashen wajen su biyu dake da cibiya a lardin Helmand na kudancin kasar a zaman wadanda ba a son ci gaba da zamansu cikin Afghanistan, kuma an ba su wa’adin kwana biyu da su fice.

Wani jami’in diflomasiyya na Turai ya ce yana fata wannan lamarin rashin fahimta ce kawai. Wani kakakin MDD ya ce ofishinsu a Afghanistan yana kokarin gano tushen wannan lamarin.

XS
SM
MD
LG