Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe tsohuwar frayim-ministar kasar Pakistan, Malama Benazir Bhutto


Mun sami labarin cewa an kashe tsohuwar frayim-ministar kasar Pakistan, Malama Benazir Bhutto. Kafofin watsa labaran Pakistan da na yammacin Turai sunce Ms Bhutto ta mutu ne daga raunukkan da ta samu a sanadin harin kunar bakin waken da aka kai a wajen taron laccar da tayi wa jawabi a Rawalpindi. Wasu rahottani kuma sunce harbe ta aka yi. Ko bayan Ms Bhutto, wasu mutane 15 su ma sun rasa rayukkansu a cikin farmakin.

XS
SM
MD
LG