Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kenya Ta Fada Cikin Fitinar Siyasa A Bayan Da Hukuma Ta Ce Shugaba Mwai Kibaki Shi Ne Ya Sake Lashe Zabe


Kenya ta fada cikin duhun fitina a sanadin tunzuri da zanga-zangar 'yan hamayya a bayan da hukumomi suka bayyana cewa shugaba Mwai Kibaki ne ya sake lashe zabe da rata 'yar kadan.

Jiya lahadi, jam'iyyar hamayya ta "Orange Democratic Movement" ta yi zargin cewa an tabka magudi. Ta yi kira ga 'yan Kenya da su hallara yau litinin a birnin Nairobi domin su ayyana Raila Odinga na jam'iyyar hamayya ta ODM a matsayin "Shugaban jama'a", amma 'yan sanda sun haramta yin wannan gangamin.

'Yan sanda suka ce duk wanda ya je shi wurin wannan gangami a dandalin da ake kira "Uhuru Park" zai dandana kudarsa a hannun hukuma.

JIya lahadi, gwamnati ta rufe watsa duk wani shiri kai tsaye lokacin da ake yinsa a gidajen rediyo da telebijin, a daidai lokacin da aka barke da yamutsi a bayan bayyana cewar Kibaki ne ya lashe zaben.

Tun da fari, adadin da aka samu na sakamakon zabe daga sassan da ba na hukumomi ba, sun nuna cewa Mr. Odinga yana kan gaba da rata mai yawa, amma kuma sai hukuma ta ce shugaban mai ci ya kamo ya kuma wuce mai kalubalantar tasa a bayan da aka kara wa'adin kwanaki biyu wajen kidayar kuri'u.

Shaidu sun ce masu zanga zanga sun kona kantuna da motoci a babban birnin kasar Nairobi, yayin da rahotanni suka ce an kashe mutane akalla 13 a tashe-tashen hankula masu alaka da zaben a Nairobi da wasu biranen kasar Kenya.

XS
SM
MD
LG