Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kenya Shugaban Adawa, Raila Odinga, ya soke zanga zangar da ya shirya yi


Shugaban Adawan Kenya Raila Odinga, ya soke zanga zangar da ya shirya yi cikin wannan mako,yana mai cewa yana so ya bada dama ga shawarwarin sulhu tukun. Shawarwar dakatar zanga zangar da ya bayar ayau litinin,yazo dab da lokacinda gwamnati ta bada sanarwar cewa tashe tashen hankula da suka biyo bayan zaben kasar ya halaka kusan mutum dari biyar.

A yau litinin ne Odinga ya gana da mukaddashiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da Africa Jendayi Frazaer,domin tattaunawa kan hanyoyin gudnarda shawarwari da zai kawo karshen fitinar siyasar cikin kasar.

Odinga yana zargin shugaban kasar Mwai Kibaki da sace zaben.Shugaban adawa yace babu tattaunawa kai tsaye da Mwai Kibaki.Amma jiya Lahadi yace a shirye yake ya tattauna muddin akwai masu shiga tsakani na kasashen ketare zasu halarci zaman shawarwarin. Shugabannin Jamiyyyar Adawa ODM ko Orange Democratic Movement a turance tayi kiran da a sake sabon zabe.Ita ma Gwamnati ta amince da haka amma tace sai idan kotun ta bada umurnin haka.

Wakiliyar MA Lisa Schlein, ta aiko mana da rahoto daga Hedkwatar Hukumar lura da masu gudun hijira ta MDD dake Geneva gameda aikewa da kayan agaji ga mutane da fitinar ta raba su da muhallansu.

XS
SM
MD
LG